Idan da ni ne Sanchez da na bar Arsenal —Ian Wright

Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sanchez ya yi sa-in-sa da wasau 'yan wasan Arsenal a filin atisaye kafin wasansu da Liverpool

Tsohon dan wasan gaba na Arsenal Ian Wright ya ce idan da shi ne a yanayin da Alexis Sanchez yake ciki yanzu a kungiyar da kila zai bar ta ne kawai.

Sanchez, mai shekara 28, ya yi sa-in-sa da abokan wasansa a kungiyar bayan da ya bar filin atisaye kafin su tashi, a lokacin da suke shirin tunkarara wasansu da Liverpool, ranar Asabar.

Wright ya ce, abin da ke faruwa yanzu tsakanin dan wasan da kungiyar ba zai amfani kulob din da dan wasan ba.

Lokacin da aka yi sa-in-sa a filin atisayen, ta kai har sai da aka rike wani daga cikin 'yan wasan na Arsenal, saboda suna neman ba wa hammata iska.

Wright ya ce, abin kunya ne saboda shi ne gwarzon dan wasan Arsenal, wanda kuma take matukar bukata a yanzu.

Ya kara da cewa, ba ya jin kudi zai sa ya zauna a kungiyar a yanzu, saboda in har zai fice daga atisaye, kuma ba ya shiga wasa.

Amma kuma ya ce, ga alama ba matsala ce ga dan wasan ba, tun da har zai yadda a sa shi wasa kuma ya shiga, sannan kuma ya dage tukuru ya yi wasan.

Tsohon dan wasan ya ce, amma fa duk da haka, idan da shi ne Sanchez, da zai tafi ne duk da haka, saboda abin da ke faruwa a Arsenal yanzu, ba abin da ya kawo shi kungiyar kenan ba, musamman ma, rashin kasancewarta cikin kungiyoyi hudu na saman teburin Premier.

Wright ya ce ga alama dan wasan ba ya jin dadin kungiyar, hankalinsa ba a kwance yake ba, kuma kamar yana son tafiya ne.