Za a sake ginin filin wasan Chelsea

Filin wasa na Stamford Bridge
Image caption Filin Stamford Bridge na yanzu yana daukar 'yan kallo 41,600

Magajin garin birnin London ya amince da bukatar Chelsea ta rushe filin wasanta na Stamford Bridge, a gina sabo na fam miliyan 500, mai kujeru 60,000.

Tun a watan Janairu ne hukumar da ke da alhakin kula da gine-gine ta birnin (Hammersmith and Fulham Council) ta amince da shirin rushe filin wasan na Stamford Bridge, mai daukar mutane 41,600.

To amma kuma magajin garin na birnin London Sadiq Khan shi ne ke da iko na karshe kan amincewa da hakan.

Tun da farko dai magajin garin ya ce sabon ginin da za a yi na zamani, mai inganci da ban sha'awa zai sa a samu kari a kan yawan kyawawan filayen wasa da ake da su a birnin.

Sadiq Khan ya kara da cewa, yana da kwarin guiwa sabon filin wasan zai zama tamkar wani tauraro a tsakanin filayen wasa na birnin London, wanda kuma zai ja hankalin masu ziyara da masu sha'awar wasan kwallon kafa daga kasashen duniya.

Kungiyar ta Chelsea ta ce ta ji dadin matakin magajin garin na amincewa da shirin nata na zamanantar da filin wasan na Stamford Bridge.

Shugaban kungiyar magoya bayan kungiyar Trizia Fiorellino, ya ce, aikin babban abin alhari ne a garesu, domin Tottenham sun yi sabon filin wasa, West Ham ma ta yi sabo, amma kuma su suna cikin hadarin barinsu a baya, amma yanzu wannan labarin ya dadada musu rai.

Hakkin mallakar hoto CHELSEAFC/HERZOG & DE MEURON
Image caption Yadda sabon filin wasan na Stamford Bridge zai kasance

Kamfanin Herzog and de Meuron, wanda ya zayyana filin wasan Olympic na Beijing, ''Birds Nest'' shi ya zayyana sabon filin wasan na Chelsea.

Daman tun da dadewa mai kungiyar ta Chelsea Roman Abramovich ya dade yana son kara yawan 'yan kallon da ke shiga filin wasan nasu.