Boksin: Bellew na duba yuwuwar ritaya bayan doke Haye

Tony Bellew Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bellew ya bayar da mamaki da ya doke tsohon zakaran ajin masu nauyi na duniya Haye

Tony Bellew ya ce yana duba yuwuwar ritaya daga damben boksin bayan da ba zato ba tsammani ya doke babban abokin hamayyarsa David Haye a filin wasa na O2 Arena da ke London ranar Asabar.

Sai dai Bellew mai shekara 34, dan yankin Liverpool ya nuna cewa idan aka neme shi da yin wani damben daya nan gaba, to kila ba zai bari damar ta wuce shi ba.

Dan boksin din ya gaya wa BBC cewa bai san ko sau nawa zai sa jikinsa da iyalinsa a cikin wannan abu ba.

Bellew wanda zakaran kambin boksin na ajin matsakaita nauyi na hukumar WBC ne, ya ba wa masu fashin baki da hasashe mamaki inda ya doke Haye, wanda ya ji rauni a agararsa a damben.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An tafi da David Haye asibiti kai tsaye bayan damben

Damben shi ne boksin din Bellew na farko na ajin masu nauyi, inda yanzu yake da tarihin nasara 29 da canjaras daya a boksin 32 da ya yi.

Bayan damben na ranar Asabar sai da aka yi wa David Haye tiyata a asibiti ta raunin da ya ji a agara.

Haye, tsohon zakaran ajin masu nauyi na duniya, mai shekara 36 ya ji raunin ne a turmi na shida, kuma a turmi na 11 aka yi masa kwab daya, abin da ya bai wa kowa mamaki.