Ibrahimovic da Mings na fuskantar haramcin wasa uku

Mings da Ibrahimovic a lokacin rigimarsu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mings da Ibrahimovic sun tsira daga hukuncin alkalin wasa Kevin a lokacin da suka yi rigimar

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta tuhumi dan wasan gaba na Man United, Zlatan Ibrahimovic da dan wasan baya na Bournemouth Tyrone Mings da laifin rigima a wasansu.

'yan wasan biyu sun yi 'yar sa-in-sa a lokacin wasan na ranar Asabar da suka tashi kunnen-doki 1-1, lokacin da Mings mai shekara 23 ya taka dan wasan gaban na Manchester United, Ibrahimovic a ka.

Daga nan ne kuma can gaba a wasan sai shi ma Ibrahimovic ya mangari Mings a fuska da gwiwar hannunsa.

An ba wa 'yan wasan biyu wa'adin zuwa karfe shida na yamma agogon GMT, ranar Talata, su bayar da bahasi kan tuhumar.

Hukumar ta FA, a sanarwar tuhumar ta ce 'yan wasan sun aikata laifukan ne a lokaci daban-daban, a kusan minti 44 na wasan, wanda a lokacin alkalin wasa da masu taimaka mi shi ba su gani ba, amma kuma an dauka a bidiyo.

Hukuncin dukkanin laifukan biyu, kora ce daga wasa (jan kati), abin da zai sa kenan a haramta wa Ibrahimovic ko Mings wasa uku, idan an same su da laifi.

Amma kuma Mings zai iya fuskantar karin haramcin wasa, saboda girman laifinsa, wanda ya aikata a lokacin da dan wasan da ya yi wa ba kwallo a wurinsa.

Domin laifi ne da wasu manyan tsoffin alkalan wasa uku, daban-daban kowanne yake yin nazarin bidiyon abin da dan wasa ya yi, sannan su sanar da hukunci, wanda sai ya zama hukunci iri daya, a aiwatar da shi.

Idan aka samu Ibrahimovic da laifi, kuma aka haramta masa wasa uku, to ba zai yi wasan dab da na kusa da karshe ba na kofin FA wanda za su yi da Chelsea da wasan Premier na Middlesbrough da kuma na West Brom, amma yana da damar yin wasannin Kofin Europa.

Shi kuwa Mings hukuncinsa in har an same shi da laifi, zai hana shi wasan Bournemouth da West Ham da na Swansea City da kuma wanda za su yi da Southampton.