Za a rika kallon wasannin Turai kyauta a shafukan sada zumunta

Real Madrid na murnar cin Kofin Zakarun Turai na 2016 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ce ta dauki kofin Zakarun Turai na 2016 a watan Mayu, bayan ta doke Atletico Madrid a fanareti

Kamfanin tashar BT Sport ya tsawaita kwantiraginsa na ikon nuna wasannin Kofin Zakarun Turai na Uefa da kuma na Europa a talabijin har zuwa shekara ta 2021 a wata yarjejeniya da ta kai ta fan biliyan 1 da miliyan dari 2.

Kamfanin shi ne yake nuna wasannin gasar manyan kungiyoyin Turai tun shekara ta 2015 a karkashin wata yarjejeniya ta fan miliyan 897 da aka kulla tun 2013.

BT Sport, dai mallakar babban kamfanin Birtaniya ne da ke samar da intanet da layin wayar salula na BT.

Tashar ta ce za ta rika sanya wasu sassa na hotunan bidiyo na wasanni da na bayanai na wasannin mako-mako da kuma wasannin karshe na kofunan Zakarun Turan na Uefa da Europa da za a rika kallo kyauta a shafukan sada zumunta.

Za a tabbatar wa manyan gasar lig-lig hudu na Turai gurbi hudu a matakin wasannin rukui-rukuni na kofin Zakarun Turai daga kakar 2018-19.

Manyan gasar lig-lig din hudu na Turai, kamar yadda hukumar kwallon kafa ta Turai ta tabbatar a yanzu su ne, Premier ta Ingila da La Liga ta Spaniya da Bundesliga ta Jamus da kuma Serie A ta Italiya.

A karkashin tsarin da ake bi yanzu Ingila da Jamus da Spaniya kowacce tana da gurbin kungiyoyi uku-uku a gasar ta Zakarun Turai, yayin da kungiyoyinsu na hudu za su yi wasan fitar da gwani kafin su samu cikon gurbi na hudu.