Ozil ba zai yi wasan Bayern Munich ba

Mesut Ozil tare da 'yan wasan Arsenal lokacin atisaye Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wenger ya ce Ozil ba zai iya wasan na Talata ba, duk da atisayen da ya yi ranar Litinin

Dan wasan tsakiya na Jamus Mesut Ozil ba zai yi wasan da Arsenal za ta yi na Kofin Zakarun Turai karo na biyu, na zagayen kungiyoyi 16 da Bayern Munich ranar Talata ba, saboda rashin lafiya.

Amma kuma kocin Arsenal din Arsene Wenger ya ce yana sa ran dan wasan mai shekara 28, ya samu sauki har ya buga wasan dab da na kusa da karshe na kofin FA da za su yi ranar Asabar da Lincoln City.

Kocin ya ce ba ya jin Ozil zai iya wasan da zakarun na Jamus duk da cewa ya shiga atisayen da suka yi ranar Litinin.

Har kawo yanzu kocin dan Faransa bai yanke shawara ko zai sa Alexis Sanchez a farkon wasan ba.

Dan wasan wanda shi ne kan gaba wajen ciwa kungiyar ta Premier kwallo a bana, inda ya zura 20 a raga, sai daga baya aka sa shi a wasan da Liverpool ta doke su 3-1 a karshen mako.

Dan Chilen mai shekara 28 ya yi sa-in-sa da abokan wasansa na Arsenal din, bayan da kwatsam ya bar atisayen da suke yi kafin wasan nasu da Liverpool na ranar Asabar, ko da yake Wenger ya musanta maganar.

Kila kuma kyaftin din kungiyar Per Mertesacker zai yi wasan na Talata, wanda zai kasance wasansa na farko a kakar nan, bayan da ya warke daga jinyar ciwon guiwar da ya ji tun a bazara.

Tsohon dan wasan na baya na kungiyar Werder Bremen mai shekara 32, ya kalli wasan da Bayern Munich din ta doke su a Allianz Arena da ci 5-1, a cikin 'yan kallo.