Kocin Napoli ya karaya a haduwarsu da Real Madrid

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kwallo biyu ya rage Cristiano Ronaldo ya ci 100 a gasar Zakarun Turai

An sa Cristiano Ronaldo da Gareth Bale cikin 'yan wasan da za su buga wa Real Madrid wasan karo na biyu na ranar Talata na Zakarun Turaia, zagayen kungiyoyi 16, da Napoli.

'Yan wasan na gaba biyu ba su taka leda a karawar La Liga da Real Madrid ta doke Eibar 4-1 a ranar Asabar ba.

Ronaldo ya samu kansa daga 'yar damuwar da ya yi fama da ita a lokacin, shi kuwa Bale yana hukuncin hana shi wasa a lokacin.

Babban dan wasansu na baya Raphael Varane ba zai yi wasan ba saboda ya ji rauni a cinya.

A karawar farko da suka yi a Madrid an ci Napoli, wadda yanzu dan wasanta na gefe Dries Mertens ya warke daga jinya 3-1.

Sau biyu Mertens ya zura kwallo a raga a wasan Serie A da suka bi Roma har gida suka doke ta 2-1 a karshen mako.

Kuma sakamakon ya sa Napolin ta rage ratar da Roman ta ba ta a matsayin ta biyu a tebur da maki biyu.

Sai dai kuma game da haduwar tasu da Real Madrid kociyansu Maurizio Sarri ya ya karaya, yana mai cewa damar kashi uku cikin dari suke da ita ta farke kwallayen da aka zura musu, har su yi nasara a filin nasu na Stadio San Paolo.