Leicester za ta ba wa Shakespeare matsayin cikakken koci

Craig Shakespeare Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shakespeare bai taba aikin cikakken kociya ba, amma tun da ya karbi jagorancin Leicester ta ci duka wasanta biyu

Za a bai wa Craig Shakespeare matsayin cikakken kocin Leicester City har zuwa karshen kakar wasan da ake ciki, kamar yadda BBC ta fahimta.

Shakespeare shi ne mataimakin Claudio Ranieri, kuma ya kasance kocin riko na kungiyar tun lokacin da aka kori dan Italiyan a watan Fabrairu.

Tun lokacin da Shakespeare ya kama aiki, masu rike da kofin Premier sun ci duka wasansu biyu.

Kocin mai shekara 53 bai taba rike mukamin cikakken koci ba, kuma wanda Ranieri ya gada, Nigel Pearson shi ne ya kawo shi Leicester.

Leicester ta kori Ranieri, mai shekara 65, wata tara bayan ya jagoranci kungiyar ta dauki kofin Premier.

Leicester ta tattauna da wasu kociyoyin da take zawarcinsu domin maye gurbinsa, ciki har da tsohon kociyan Ingila Roy Hodgson.

Wasan farko da Shakespeare ya jagoranci kungiyar a matsayin kocin rikon kwarya, ta doke Liverpool 3-1.