Cardiff: Burinmu shi ne komawa Premier

Vincent Tan dan Malaysisa mai kungiyar Cardiff City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Vincent Tan dan kasuwar Malaysia shi ne ya mallaki kungiyar ta Cardiff City

Kungiyar Cardiff City ta yi asarar kusan fan miliyan tara da rabi a zuwa watan Mayu na karshen shekarar 2016, idan aka kwatanta da abin da ribar da ta samu ta kusan fan miliyan hudu a shekara ta 2015, kamar yadda alkaluman kudi na kungiyar suka nuna.

Kudaden da kungiyar ke samu daga masu shiga kallon wasanta da watsa wasanninta ta talabijin da sauran kafofi da tallace-tallace da sauran hanyoyin kasuwanci, sun ragu daga sama da fan miliyan 37 zuwa sama da fan miliyan 31.

An kuma rage albashi da alawus din 'yan wasanta daga fan miliyan 30.8 zuwa fan miliyan 25.4

Alkaluman sun nuna asarar fan miliyan 9.469, amma kuma a sanarwar da kungiyar ta bayar ta ce duk da haka za ta ci gaba da zuba jari.

Babban jami'in kungiyar Ken Choo, ya ce, babban burinsu shi ne komawa gasar Premier kawai ba tare da bata wani lokaci ba.