An dakatar da Ibrahimovic wasa uku

Mings and Ibrahimovic went unpunished by referee Kevin Friend for the incidents where they clashed Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Alkalin wasa Kevin Friend bai hukunta 'yan wasan ba a lokacin da abin ya faru

Zlatan Ibrahimovic ya amince da hukuncin da aka yi masa na hana shi wasa uku, saboda mangarar da ya yi wa dan wasan baya na Bournemouth Tyrone Mings da guiwar hannu lokacin da suka yi 1-1 ranar Asabar a Old Trafford.

Dan wasan gaban na Manchester United ba zai buga wasansu na dab da na kusa da karshe ba na Kofin FA, wanda za su yi da Chelsea ranar Litinin.

Haka kuma ba zai taka leda a wasannin Premier da Manchester United za ta yi da Middlesbrough da kuma wanda za ta yi da West Brom ba.

Shi ma Mings hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Ingila FA, ta tuhume shi da aikata laifin da ya saba wa dokokin wasan, amma kuma Bournemouth ta ce za ta daukaka kara kan tuhumar dan wasan nata na baya.

Ibrahimovic, wanda shi ne kan gaba wajen ci wa United kwallo a bana, inda ya zura kwallo 26, yana da damar buga wasan kofin Europa da United za ta yi a gi dan Rostov ta Rasha ranar Alhamis.

Shi da wasan Premier sai lokacin karawarsu da Everton ranar 4 ga watan Afrilu.

Mings, mai shekara 23, ya taka Ibrahimovic ne mai shekara 35 a ka, kafin minti daya tsakani shi ma dan wasan gaban na United ya mangare shi a fuska da guiwar hannu lokacin da suka tashi sama a wani bugun gefe da aka yo.

An ba wa 'yan wasan biyu wa'adin karfe bakwai na yamma agogon Najeriya na Talatar nan su bayar da bahasi kan tuhumar.