Lalata :Tsohon Jami'in Man City na fuskantar tuhuma

Barry Bennell Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Ana tuhumar Barry Bennell da lalata da matasan 'yan wasansa lokacin yana kociya

An tuhumi tsohon kociyan kungiyar Crewe Alexandra, Barry Bennell, wanda ya taba aiki da Manchester City da Stoke City, da laifin lalata da yara.

Tsohon kociyan na fuskantar tuhuma takwas ne, kan laifukan da ake zargi ya aikata a kan matasan 'yan wasansa tun a wasu shekarun baya.

Ana zargin tsohon kociyan matasan na Crewe Alexandra mai shekara 63 da lalata da yara biyu tsakanin shekarar 1980 da 1987, da kuma wasu laifukan biyar.

Daya daga cikin yaran a lokacin yana kasa da shekara 14 ne yayin da dayan yake kasa da shekara 16.

A ranar Litinin 13 ga watan Maris ne Mr Bennell zai gurfana a gaban kotun majistare ta South Cheshire.