Barcelona za ta iya cin PSG 6—Enrique

Luis Suarez da sauran 'yan wasan Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Luis Suarez (a tsakiya ), ya ce sun san tsaka-mai-wuyar da suke ciki, amma a kwallon kafa komai na iya faruwa

Luis Enrique ya ce yana da kwarin guiwa Barcelona za ta iya cin kwallo 6 ta kafa tarihi a gasar Kofin Zakarun Turai, ta yi galaba a kan PSG wadda ta ci ta 4-0, a wasansu na farko.

Sati biyu da ya wuce Barca ta sha kashi 4-0 a gidan Paris St-Germain a wasan nasu na zagayen kungiyoyi 16 karon farko, wanda a yanzu suke son ganin sun yi abin da ba wata kungiya da ta taba yi.

Enrique ya ce a cikin minti 95 abubuwa masu yawa za su iya faruwa, saboda haka ya yi amanna za su kasance dab da tsallakewa.

Ya kara da cewa ba wai yana cewa za su tsallake ba ne, amma za su kasance kusa, kuma idan Psg za ta ci su 4, su ma za su iya cinsu 6.

Zakarun na Spaniya sun ci kwallo 11 a wasansu biyu na karshen nan, kuma kwallo daya kawai aka zura musu a raga.

Shi kuwa Luis Suarez cewa ya yi, suna sane da irin mawuyacin halin da suke ciki, to amma a wasan kwallon kafa ba abin da ba zai iya faruwa ba.

Bayanai akan Wasan:

-Ba wata kungiya da ta taba farfadowa ta yi nasara bayan an ci ta 4-0 a waje a wasan farko na matakin sili-daya-kwale na gasar Kofin Zakarun Turai.

-lokaci daya da PSG ta fitar da Barcelona a gasar Zakarun Turai, shi ne wasan dab da na kusa da karshe na 1994-95(3-2 jumulla).

-Tun daga sannan a haduwarsu biyu Barcelona ta fitar da kungiyar ta Paris a 2012-13 da 2014-15.

-A shekara tara Barcelona ta wuce wannan matakin na kungiyoyi 16, abin da ba wata kungiya da ta taba yi a gasar. Lokacin da ta kasa kaiwa wasan dab da na kusa da karshen shi ne lokacin da Liverpool ta fitar da su a 2006-07.