Europa: Mourinho ya yi korafi kan filin da za su yi wasa da Rostov

Filin wasan Rostov, Olimp-2 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rostov ta shirya barin filin wasan na Olimp-2 bayan gasar cin Kofin Duniya ta 2018 a Rasha

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya yi suka a kan filin da kungiyar tasa za ta yi wasan Kofin Europa da Rostov ta Rasha ranar Alhamis.

Rostov, wadda ke matsayi na biyar a gasar lig din Rasaha, tana wasa ne a filin Olimp-2, wanda aka gina a 1930, kuma yana daukar 'yan kallo sama da 15,000 kawai.

Kafin wasan nasu na farko na zagayen kungiyoyi 16, Mourinho ya ce da wuya ya yadda cewa a wannan fili za su yi wasa, idan har ma za ka iya kiransa fili.

Mourinho ya kwatanta yanayin filin, da wanda aka tsara United za ta yi wasan sada zumunta na kafin kaka da Manchester City a Beijing ta China, wanda aka fasa saboda rashin kyawunsa.

Kocin dan Portugal ya ce yanayin filin zai shafi zaben 'yan wasan da zai iya sawa a wasan.

Ya ce dan wasansa na tsakiya dan Armenia, Henrikh Mkhitaryan ya warke daga jinyar da ya yi ta ciwon cinya, abin da ya hana shi wasa biyu, amma kocin ya ce bai sani ba ko zai yi kasadar sa shi.

A watan Disamba, Mourinho ya nuna bacin ransa kan yadda Uefa ta sa United ta yi wasan Europa na matakin rukuni a Zorya Luhansk a fili mai kankara.

Mourinho ya ce a lokacin da yake duba filin ya yi magana da wani jami'in Uefa, amma da ya nuna masa damuwarsa kan yanayin filin sai, mutumin ya ce masa ba komai ko da wani abu ya samu wani dan wasa, saboda an yi musu inshora.