Wenger ya ce alkalin wasansu da Bayern ya harzuka shi

Arsene Wenger cikin damuwa Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Wannan shi ne wasa na 201 na Zakarun Turai da Arsene Wenger ya jagoranci Arsenal

Arsene Wenger ya ce alkalin wasan da ya jagorancin wasan da Bayern ta casa su a Emirates, ya harzuka shi, amma kuma kocin ya ce yana alfahari da 'yan wasan nasa.

Alkalin wasa Anastasios Sidiropoulos ya ki ba wa masu masukin bakin fanareti, lokacin sun ci 1-0, amma kuma daga bisani ya ba wa bakin fanareti kan yadda Laurent Koscielny ya tunkari Robert Lewandowski a wani hari da ya kawo.

Bayan fanaretin alkalin wasa ya ba wa Koscielny katin gargadi, amma kuma bayan ya gana da daya daga cikin mataimakansa, sai ya ba shi jan kati, wato ya kore shi.

A kan wannan ne Wenger ya ce, bai ga dalilin fanaretin da korar da aka yi wa dan wasan ba, ya kara da cewa abin da alkalin wasan ya yi tsabar rashin sanin ya kamata ne.

Arsenal ta yi wasan ne na ranar Talata wanda aka doke ta 5-1, cikin matsi kasancewar daman Bayern din ta casa su 5-1, a wasan farko da suka yi mako uku da ya wuce.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tarin wasau magoya bayan Arsenal da ke zanga-zangar neman kocin ya tafi, kafin wasan a kofar Emirates

Kocin dan Faransa mai shekara 67, ya fuskanci bore daga magoya bayan kungiyar kafin wasan a Emirates, inda suke nemansa da ya sauka daga aiki.

Amma kuma da aka tambaye game da boren magoya bayan, sai ya ce ba shi da abin da zai kara a kai.

Yanzu dai sau bakwai a jere kenan ana fitar da Arsenal daga gasar ta Zakarun Turai a wannan matakin.

Tsohon dan wasan tsakiya na Tottenham Jermaine Jenas ya ce, abin da zai fi kyau shi ne Wenger ya hakura da aikin bayan shekara 21 da ya yi a kungiyar.