A tuhumi 'yan wasan Arsenal ba Wenger ba - Rachel Yankey

Wasu magoya bayan Arsenal na masu son ganin Wenger ya tafi Hakkin mallakar hoto Allsport
Image caption Wasu magoya bayan Arsenal da ke neman ganin Arsene Wenger ya bar kungiyar haka

Tsohuwar kyaftin din kungiyar Arsenal ta mata Rachel Yankey ta ce an bar jaki ne ana bugun taiki game da sukan da ake yi wa Arsene Wenger kan halin da Arsenal ke ciki, na rashin tabuka abin kiriki.

Yankey ta ce duk wadannan maganganun da ake yi, idan aka kori Arsene Wenger, me za a yi kuma a gaba? Wa za a kawo? Ina kungiyar za ta nufa?

Ta ce ita a wurinta, maganar wa ye kocin kungiyar, ta kare ainahin matsalolin da suka addabi kungiyar.

Tsohuwar kyaftin din ta ce, kamat ya yi kungiyar ta fi haka, to amma abin takaicin an dora komai a kan Wenger, wanda kuma a zahirin gaskiya 'yan wasa ne ke da alhakin abin da ke wakana a cikin fili.

Idan abubuwa suka baci, za ka so ka ga 'yan wasa sun tashi tsaye, suna bayar da himma, kowa yana iya kokarinsa. To amma ba ma ganin suna yin hakan a wasannin yanzu.

Yankey ta kara da cewa, ba su san gaba daya labarin abin da ya faru da Alexis Sanchez ba, amma wai maganar a ce an samu sa-in-sa tsakanin 'yan wasa a lokacin atisaye?

Ta ce ai wannan ba wani abu ba ne mai tayar da hankali.