Yaushe za a samu mace kociyar babbar kungiyar maza?

Rachel Yankey a lokacin da take yi wa Ingila wasa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rachel Yankey ta yi wa Ingila wasa 129, kuma ta ci kwallo 19

Tsohuwar 'yar wasan kwallon kafa ta Arsenal da Ingila Rachel Yankey ta ce za a dau lokaci kafin a samu mace mai horad da babbar kungiyar 'yan wasa maza, wasau wasu matsaloli da dama.

Tsohuwar kyaftin din ta Arsenal ta ce akwai dalilai da dama da suka sa ba a samun kociyoyi mata, amma hatta ita kanta ba za ta ce ta san su duka ba.

Ta ce abu na farko ya shafi bambancin da ake nuna wa mata ne, ta yadda ake kin daukarsu aiki ko da kuwa suna da kwarewa.

Yankey ta kara da cewa za ta iya kwatanta wannan da irin kalubalen da koci-koci bakar fata ke fuskanta wajen samun aiki, ta ce ya kamata a samu sauyi a dabi'ar hakan.

Yankey wadda yanzu take da takardar hukumar kwallon kafa ta Turai ta kwarewa ta biyu a aikin koci, ta ce duk da irin ci gaban da ake samu na mata a wannan fanni na aikin koci,har yanzu ana nuna wa mata bambanci a harkar kwallon kafa, kuma muddin ba a kawar da hakan ba, abu ne mai wuya a samu mace kocin wata babbar kungiyar kwallon kafa ta maza.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A Arsenal Yankey ta dauki kofin lig 8, da kofin FA 9, da kuma kofin Zakarun Turai na mata daya

Tsohuwar 'yar wasan ta ce to amma duk da haka idan aka waiwayi baya za a ga akwai cigaba sosai a fagen kwallon kafar mata.

Ta ce lokacin da take karama ta taba aske gashinta, domin a dauka ita namiji ce, don kada wani ya ce me tambaye ta dalilin da take kwallon kafa.

Kuma ta ce a lokacin da take koyar da wasan a makarantun framare a shekara ta 2004, sai yaran kawai su ga mace ta zo musu fili, sai ka ji suna cewa: ''Ah! Ya aka yi mace ce kociyanmu?'' Ta ce to amma yanzu duka ba wannan.

Yankey ta ce, to amma duk da wannan cigaba tana ganin abu ne da zai dauki lokaci kafin a samu mace ta zama mai horad da babbar kungiyar wasa maza, saboda wasu abubuwa na waje da za su iya tasiri a kanka.

Ta ce dubi yadda magoya baya da 'yan jarida ke yi wa kocin Arsenal Arsene Wenger ko tsohon kocin Leicester Claudio Ranieri. Yankey ta ce to da ace mace ce a wannan aiki ya abin zai kasance? Ta kara da cewa aikin koci yana da kalubale da dama.