FA ta haramta wa Tyrone Mings na Bournemouth wasa 5

Tyrone Mings da Zlatan Ibrahimovic a lokacin wasan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mings ya nemi sa-in-sa da Ibrahimovic a lokacin wasan na ranar Asabar, wanda aka tayar da jijiyar wuya

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta haramata wa dan wasan baya na Bournemouth Tyrone Mings wasa biyar saboda samunsa da laifin taka dan wasan gaba na ManUnited Zlatan Ibrahimovic a ka.

Dan wasan mai shekara 23 ya yi wa Ibrahimovic ketar ne a lokacin wasan da suka tashi kunnen doki 1-1 ranar Asabar a Old Trafford.

Shi ma Ibrahimovic jim kadan da yi masa ketar, ya rama inda ya mangari Mings da guiwar hannu a fuska, kuma shi ma FA din ta yi masa hukuncin haramcin wasa uku, hukuncin da ya ce ya karba.

To amma a nata Bournemouth ta ce hukuncin da FA din ta yi wa dan wasan nata na baya, abin takaici ne matuka, wanda ba ta yi tsammani ba.

Yanzu Mings ba zai yi wa Bournemouth wasanya biyar ba na gaba, amma zai dawo fili a wasan da za su ziyarci Tottenham ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, kuma rashin nasa zai kara matsalar 'yan baya da kungiyar ke fama da ita.

Bournemouth tana matsayi na 14 a tebur da maki biyar tsakaninta da rukunin 'yan faduwa daga gasar ta Premier.