A Jamus ko Turkiyya za a yi gasar Kofin Kasashen Turai ta 2024

'Yan wasan Portugal da suka ci kofin Turai na gasar 2016, a Faransa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Portugal ce ta dauki kofin gasar Turai ta 2016, wadda aka yi a Faransa

Hukumar kwallon kafa ta kasashen Turai, Uefa, ta tabbatar da cewa a Jamus ko Turkiyya za a yi gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Turai ta 2024.

Kasashen biyu ne kadai suka mika takardun bukatarsu ta neman karbar bakuncin gasar kafin wa'adin da aka gindaya na ranar uku ga watan Maris.

Kasashen Denmark da Norway da Sweden da Finland sun yi niyyar neman karbar bakuncin gasar na hadaka, amma kuma har karshen wa'adin ba su gabatar da bukatar tasu ba.

A yanzu dai kasashen biyu na Jamus da Turkiyya za su gabatar da takardun cikakkun bayanan irin tanadin da suke da shi na karbar gasar, nan da watan Afrilu na 2018, inda hukumar ta Uefa za ta zabi wadda ta fi cancanta a tsakaninsu a watan Satumba na shekarar.

Za a dawo da tsarin gudanar da gasar a kasa daya kawai, bayan an yi ta shekarar 2020, wadda za a yi a birane 13 na nahiyar Turai.

Jamus ta Yamma ta karbi bakuncin gasar Kofin Duniya ta 1974 da gasar Kofin kasashen Turai ta 1988, sannan kuma bayan kasashen Jamus din biyu ta Yamma da ta Gabas sun hade, aka yi gasar Kofin Duniya ta 2006 a can.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Jamus Reinhard Grindel ya ce yana da kwarin guiwa za su iya gudanar da gasa mai armashi sosai, saboda irin kwarewa da kayayyakin da suke da su da kuma kyakkyawan yanayin kasar.

Turkiyya ba ta taba karbar bakuncin wata babbar gasa ba, bayan da ta kasa samun damar hadin guiwa da Girka ta karbar gasar Kofin Turan ta 2008, da kuma neman tata ita kadai ta 2012.

Shugaban hukumar kwallon kafar ta Turkiyya Yildirim Demiroren, yana fatan za su yi nasarar samun damar a karo na uku.