An tuhumi Arsenal da Bayern kan rashin da'ar 'yan kallo

Ma'aikata na kokarin gayar filin Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An tsayar da wasan a mintin farko, domin kwashe abubuwan da magoya bayan na Bayern suka jefa

Hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa, ta tuhumi Arsenal da Bayern Munich da laifin rashin da'ar magoya bayansu a wasan Kofin Zakarun Turai karo na biyu na zagayen kungiyoyi 16 a Emirates.

An tuhumi Bayern ne da laifin jefa abubuwa cikin fili, bayan da magoya bayanta suka sa aka jinkirta wasan lokacin da suka rika jefa irin takardar nan da ake amfani da ita a bandaki.

Magoya bayan na kungiyar ta Jamus suna korafi ne akan tsadar tikitin shiga kallon wasan.

Ita ma Arsenal an tuhume ta da laifin kutsen da wani mai goyon bayanta ya yi a cikin fili a wasan na biyu da aka doke ta da ci 5-1, sakamakon da ya zama 10-2 gida da waje.

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Dan wasan baya Bayern Rafinha shi ma ya taimaka wajen gayra filin

Napoli ma na fuskantar tuhuma ta aikata laifi a wasan da Real Madrid ta casa su 6-2 gida da waje a filinsu na Stadio San Paolo ranar Talata.

Kungiyar ta Italiya na fuskantar tuhuma hudu; ta amfani da 'yar mitsitsiyar cocilan din nan mai masifar haske, da tare hanyar da 'yan wasa ke fitowa da jefa abubuwa cikin fili da kuma kunna abubuwan tartsatsin wuta.

A ranar 23 ga watan Maris ne Hukumar kwallon kafar ta Turai za ta yi hukunci a kan laifukan.