Ibrahimovic zai fi kowa albashi a tarihin gasar Amurka idan ya je LA Galaxy

'Yan wasan LA Galaxy Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption LA Galaxy sun fi kowace kungiya cin kofin gasar Amurka, inda suka dauka sau biyar

LA Galaxy ta ce za ta biya Zlatan Ibrahimovic albashin da ya fi na kowane dan wasa yawa a tarihin gasar Amurka idan ya yarda ya koma kungiyar daga Manchester United a bazaran nan.

Ibrahimovic ya koma Manchester United ne akan yarjejeniyar shekara daya amma kuma yana da damar kara wata shekarar.

Yayin da Manchester United din ke fatan ganin ta rike dan wasan na Sweden mai shekara 35, har yanzu bai amsa cewa zai tsaya ba.

A bana Ibrahimovic ya ci wa Manchester United kwallo 26.

Duk da cewa zai yi wasan Kofin Europa na ranar Alhamis na zagayen kungiyoyi 16, karon farko wanda Manchester United za ta je gidan Rostov, an yi masa hukuncin haramcin wasa uku a gasar Ingila, kan laifin yi wa dan wasan Bournemouth gula a fuska a wasansu na ranar Asabar a Old Trafford.

A 2016, dan wasan gaba na Brazil Kaka shi ne ya fi kowane dan wasa alabashi a gasar kwallon kafar ta Amurka, inda Orlando City ke ba shi dala miliyan 7.167 a shekara.

A kakar da wuce LA Galaxy kuwa ta rika biyan tsohon dan wasan Ingila Steven Gerrard dala miliyan 6.1 a shekara, kuma tuni ya yi ritaya