Xabi Alonso zai yi ritaya daga kwallon kafa

Alonso dauke da Kofin Kasashen Turai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alonso ya dauki Kofin Kasashen Turai da Spaniya a 2008 da 2012

Dan wasan tsakiya na Bayern Munich Xabi Alonso ya tabbatar da cewa zai yi ritaya idan kwantiraginsa ya kare a karshen kakar wasan da ake ciki.

Dan wasan na Spaniya mai shekara 35, ya sanya hotonsa a shafin Twitter, yana alamar ban kwana, tare da dan takaitaccen rubutun da ke nuna cewa yana ban kwana da wasan da yake sha'awa.

Hakkin mallakar hoto XABI ALONSO/TWITTER
Image caption Sanarwar da Alonso ya sanya ta yin ritaya daga wasan kwallon kafa a shafin Twitter

Alonso ya dauki kofuna da Liverpool da Real Madrid da Bayern Munich, sannan ya dauki Kofin Duniya da kuma na Zakarun Turai biyu.

Dan wasan ya sheda wa tashar talabijin din kungiyar Bayern cewa, shawara ce mai wuya, amma kuma lokacin da ya dace kenan ya yi hakan.

Alonso ya koma Liverpool ne daga Real Sociedad a 2004, kuma yana daga cikin 'yan fitacciyar tawagar kungiyar ta Ingila da ta dauki Kofin Zakarun Turai a birnin Santambul, a shekararsa ta farko, a lokacin da Liverpool din ta farfado daga ci 3-0 bayan rabin lokaci, ta doke AC Milan a fanareti.

A 2009 ne ya koma Real Madrid kuma ya dauki Kofin Zakarun Turai na biyu da kuma kofin gasar Spaniya, kafin ya koma Jamus a 2014, inda ya taimaka wa Bayern ta dauki kofin gasar Bundesliga biyu.

Sannan kuma Bayern din ta kai wasan dab da na kusa da karshe na gasar Zakarun Turai na shekaran nan, sakamakon nasara da suka yi ta doke Arsenal 10-2 jumulla, gida da waje, ranar Talata.

Alonso ya kuma yi wa kasarsa Spaniya wasa 114, inda ya ci mata kwallo 16, inda suka dauki kofin kasashen Turai na 2008 da na 2012 da kuma Kofin Duniya da suka392193163921931639219316 dauka a Afirka ta Kudu a 2010.

Ya yi wa kasar tasa wasan karshe ne a gasar cin Kofin Duniya ta 2014 a Brazil.