Kofin Europa: Mourinho ya ajiye Wayne Rooney

Wayne Rooney
Bayanan hoto,

Wayne Rooney na fama da koma-baya a wasansa

A ranar Alhamis din nan ne za a yi wasanni takwas na cin kofin kwallon kafa naTurai na Europa, karon farko na zagayen kungiyoyi 16, inda Man United za ta kara da FC Rostov ta Rasha.

A wasan, Rostov tana gida da Manchester United din, wadda za ta yi wasan ba tare da dan bayanta ba Eric Bailly, wanda aka kora, a wasansu na baya da Saint-Etienne.

Shi kuwa kyaftin din United Wayne Rooney da dan wasansu na baya Luke Shaw ba a tafi da su ba, suna gida.

Dan wasan tsakiya dan Armenia Henrikh Mkhitaryan na iya dawowa fagen wasa bayan jinyar ciwon cinya.

United ta yi tattakin nisan mil 2,100 domin fafatawa da kungiyar wadda bayan tana matsayi na biyar a gasar lig din Rasha, sau daya kawai aka doke ta a wasanni 7 da ta yi na karshe na gasar Turai a gidanta.

Rostov din za ta yi wasan na Alhamis ne bayan ta yi nasara 6-0 a wasanta na karshen mako, yayin da United za ta yi fafatawar bayan da ta yi 1-1 da Bournemouth mai 'yan wasa 10 a lokacin.

Tun da farko kocin Manchester United Jose Mourinho ya koka da hadin wasan, bayan filin wasan nasu da ya ce bai cancanci a ma kira shi fili ba, inda ya ce ta ko ina abin bai yi ba. Ya ce wuri ne mai nisa, ga wuya, kuma wasan ya zo musu a lokacin da bai dace musu ba.

Sauran wasannin su ne:

FC Copenhagen da Ajax

Celta Vigo da FK Krasnodar

Schalke da B Gladbach

KAA Gent da KRC Genk

Lyon da Roma

Olympiakos da Besiktas