Abubuwan kara kuzari: An ci tarar Bournemouth fan dubu 35

Filin wasan Bournemouth Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An samu Bournemouth da laifin saba dokar FA ta 14 (d)

Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA ta ci tarar Bournemouth fan dubu 35 kwatankwacin sama da naira miliyan 19, bayan da kungiyar ta amince da tuhumar da aka yi mata ta saba dokokin amfani da abubuwan kara kuzari a wasa.

An tuhumi kungiyar ta Premier ne bayan sau uku ta kasa bayar da cikakken bayani kan inda 'yan wasanta suke.

A ka'ida dai kungiyyoyi suna bayar da cikakken bayani na atisayensu da kuma inda 'yan wasansu suke, domin za a iya zuwa yi musu gwajin amfani da abubuwan kara kuzari a kowane lokaci, a ziyarar bazata.

Hukumar ta FA ta kuma gargadi kungiyar kan ta gyara halinta a gaba.

An gano cewa wani fanni na tuhumar ya shafi wani dan wasa ne da bai gaya wa kungiyar adireshin sabon gidan da ya koma ba, yayin da wani bangaren laifin kuma ya shafi 'yan wasan kungiyar ne 'yan kasa da shekara 21, da suka yi atisaye da 'yan wasan babbar kungiyar, ba tare da sanar da hukumar ba a lokacin da ya dace.

Ita ma Manchester City a watan Fabrairu, an taba yi mata irin wannan tuhuma tare da cin tararta fan dubu 35, da kuma gargadinta kan ta guji sake aikata laifinand.