Ben Davies ya sabunta kwantiragi da Tottenham

Ben Davies lokacin da ya ci Aston Villa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwallon da Ben Davies ya ci wa Tottenham guda daya, ita ce ta lokacin da suka doke Aston Villa 2-0 a wasan kofin FA, zagaye na uku

Dan wasan Tottenham na baya Ben Davies ya sanya hannu a sabon kwantiragin da zai sa ya zauna a kungiyar har shekara ta 2021.

Dan wasan mai shekara 23 ya koma Tottenham din ne daga Swansea a 2014, kuma ya yi mata wasa 68 a gasa daban-daban.

Dan wasan na yankin Wales ya ce kungiya ce mai ban mamaki, wadda abin alfahari ne ka kasance a cikinta a wannan lokaci, kuma za ka ga tana ci gaba ne kawai.

Ya ce idan da a farkon lokacin da ya fara wasa ne ka ce masa zai samu wannan damar da sai abin ya daure masa kai, domin ba zai yarda ba.