Kofin Europa: Man Utd ta yi 1-1 da Rostov

Henrikh Mkhitaryan a lokacin da ya zura kwallo ragar Rostov Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Henrikh Mkhitaryan ya ci kwallonsa ta uku ta gasar Europa kenan a bana

Manchester United ta tashi kunnnen doki da FC Rostov a wasansu na farko na zagayen kungiyoyi 16 na kofin Europa, a Rasha.

An yi wasan ne a filin kungiyar ta Rasha, Olymp-2 Stadium, filin da Jose Mourinho ya nuna damuwarsa a kan rashin kyawunsa tun kafin wasan.

Sai dai United din ta yi nasarar jefa kwallo a gidan masu masaukin nata, ta hannun Henrikh Mkhitaryan a minti na 35 bayan da Fellaini ya jawo wata kwallo, wadda ya zura wa Zlatan Ibrahimovic, shi kuma ya saita wa dan wasan na Armenia.

Rostov ta farke kwallon bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, a minti na 53 ta hannun tsohon dan wasansu Aleksandar Erokhin.

Sakamakon wasan ya nuna kungiyar ta Rasha wasa daya kawai aka doke ta a cikin takwas da ta yi na gasar Turai a gidanta.

Rostov ta samu shiga gasar ta Europa ne bayan ta zama ta uku a rukuninsu na gasar Kofin Zakarun Turai ta Uefa, a bayan Atletico Madrid da Bayern Munich.

Kungiyar ta doke zakarun Turai Bayern Munich a Rasha, ko da yake wannan ita ce nasarasu daya kawai a wasa shida na kofin na Uefa.

Yanzu za a yi wasan karo na biyu a gidan Manchester United, Old Trafford, a ranar Alhamis mai zuwa da karfe tara saura kwata agogon Najeriya.

Ga sakamakon wasu daga cikin wasannin kofin na Europa na ranar Alhamis:

FC Copenhagen 2-1 Ajax

Apoel Nic 0-1 Anderlecht