U 20: Senegal za ta yi wasan karshe da Zambia

Babban filin wasa na Heroes National Stadium da ke Lusaka, a Zambia Hakkin mallakar hoto KENNEDY GONDWE
Image caption Za a yi wasan karshen ne a babban filin wasa na Heroes National Stadium da ke Lusaka, a Zambia

Senegal ta kai wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afirka ta kwallon kafa ta 'yan kasa da shekara 20, wadda ake yi a Zambia, bayan ta doke Guinea 1-0.

Duk da cewa 'yan Guinean sun fi rike kwallo da kai hari a wasan da suka yi ranar Alhamis Senegal ta yi nasarar jefa kwallo a raga ta hannun dan wasanta Aliou Badji, a minti na 12 da wasa.

A ranar Lahadi Zambia mai masaukin baki wadda ta yi waje da Afirka ta Kudu za ta kara da Senegal din a wasan karshe, a babban filin wasa na kasar da ke Lusaka.

Dukkanin kasashen biyu na Zambia da Senegal din ba wadda ta taba daukar kofin gasar.

Amma kafin wasan na karshe, Guinea za ta fafata da Afirka ta Kudu, domin neman matsayi na hudu a gasar, aranar Lahadin.

Dukkanin kasashen hudu sun samu damar zuwa gasar cin Kofin Duniya ta 'yan kasa da shekara 20, wadda za a yi a Koriya ta Kudu daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa 11 ga watan Yuni na wannan shekara.