Za mu shiga makon sanin matsayinmu- Guardiola

Pep Guardiola yana bayar da umarni lokacin wasansu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pep Guardiola yana ganin wasansu da Monaco da kuma na Liverpool su ne za su nuna yadda za su kare kakar bana

Kociyan Manchester City Pep Guardiola ya ce a yanzu suna shirin shiga makon a-yi-ta-ta-kare, wanda za su san matsayinsu a bana, a wasannin da za su yi na Monaco da kuma Liverpool.

Kociyan ya ce wasan da za su yi na Kofin Zakarun Turai da Monaco ranar Laraba 16 ga wata da kuma wanda za su yi na Premier da Liverpool ranar Lahadi 19 ga watan, su ne za su fayyace matsayinsu a wannan kakar.

Guardiola ya ce, dole ne ka dage da kyau, duk wasan da za ka yi ka nuna wa abokin karawarka cewa ka je ne domin ka yi nasara.

Ya ce wannan ita ce hanya kadai da za ka ci gaba a matsayin kungiyar da ta san abin da ya kamata, kuma wannan shi ne abin da zai yi kokarin yi a lokacinsa a kungiyar.

Kocin dan Spaniya ya ce, ba ruwansa da kowace gasa ce, ba wani korafi da wani zai yi, ko wata nadama. Mafita kawai ita ce ka je wasa kuma ka yi kokari ka ci wasan.

City wadda ta yi nasarar zuwa wasan kusa da karshe na gasar Kofin FA, bayan da ta ci Middlesbrough 5-3 ranar Asabar, za ta je karo na biyu na Kofin Zakarun Turai zagayen kungiyoyi 16 da Monaco a ranar Laraba 16 ga watan Maris.

Daga nan ne kuma kungiyar wadda take ta uku a teburin Premier, da tazarar maki 10 tsakaninta da ta daya Chelsea, yayin da ya rage wasa 11 a gama gasar, za ta karbi bakuncin Liverpool wadda take ta hudu a tebur, ranar Lahadi, 19 ga watan Maris.

Ana ganin damar da Guardiola yake da ita ta daukar kofi a shekararsa ta farko a matsayin kociyan kungiyar, ita ce ta gasar Kofin FA da kuma kofin Zakarun Turai.