Kofin FA: Tottenham ta kai wasan kusa da karshe bayan ta ci Millwall 6-0

Son Heung-min lokacin murnar daya daga cikin kwallo uku da ya ci

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Son Heung-min ya yi wa Millwall ruwan kwallo uku rigis daga cikin shida da Tottenham ta zura a ragar bakin

Tottenham ta kai wasan kusa da karshe na gasar cin Kofin FA, bayan da ta lallasa kungiyar Millwall ta gasar kasa da Premier ta League One 6-0.

Sau uku dan wasan Spurs Son Heung-min yana daga raga a wasan da suka samu samu damar zuwa matakin na gaba cikin sauki, amma kuma gwanin dan wasansu na gaba Harry Kane ya ji rauni a kafa.

Christian Eriksen wanda ya shigo domin maye gurbin dan wasan na Ingila, minti bakwai da fara wasa, shi ne ya fara jefa kwallo a raga a minti na 31 da fara taka leda.

Daga nan ne kuma sai aka fara yi wa bakin ruwan kwallo, inda Son Heung-min ya ci ta biyu a minti 41, sannan kuma ya kara ta uku bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, a minti na 54.

Dele Alli ne ya biyo baya da ta biyar a minti na72, kafin Janssen shi ma ya samu damar jefa tasa, wadda ta zamo ta biyar a minti 79.

Ana shirin tashi ne kuma bayan minti 90 na wasan sai Son ya ci wa Tottenham ta shida wadda ita ce ta ukunsa da ya jefa a raga a wasan na ranar Lahadi.

Da wannan nasara yanzu Spurs ta bi layin abokan hamayyarta na Premier Manchester City da Arsenal zuwa wasan kusa da karshe, wanda za a fitar da jadawalinsa ranar Litinin a Stamford Bridge, bayan wasan dab da na kusa da karshe tsakanin Chelsea da masu rike da Kofin na FA, Manchester United.

Tottenham din na fatan samun sauyi bayan ta yi rashin nasara a wasanninta na kusa da karshe na Kofin FA guda sau shida, inda a wannan karon suke kokarin ganin sun dauki wani babban kofi a karon farko tun shekara ta 2008.