Leicester ta nada Craig Shakespeare cikakken kociyanta

Asalin hoton, Getty Images
Shakespeare (a hagu) bai taba aikin cikakken koci ba, kuma Nigel Pearson wanda Ranieri ya gada shi ya kawo shi Leicester
An nada Craig Shakespeare a matsayin cikakken kociyan Leicester City har zuwa karshen kakar wasannin da ake ciki.
Shakespeare mai shekara 53, na zaman kocin rikon-kwarya ne tun bayan da kungiyar ta sallami Claudio Ranieri ranar 23 ga watan Fabrairu, wata tara bayan daukar kofin Premier.
Shi dai Shakespeare, wanda bai taba rike aikin cikakken kociya ba, shi ne mataimakin Ranieri, bayan da wanda ya gabaci dan Italiyan, Nigel Pearson ya kawo shi kungiyar.
Tun lokacin da aka ba shi aikin rikon-kwaryar Leicester ta ci duk wasanta biyu, inda da farko ta ci Liverpool 3-1, kamar yadda ta yi wa Hull City ma a wasan na biyu.
Kungiyar wadda ke rike da kofin Premier tana matsayi na 15, maki uku tsakaninta da rukunin faduwa daga gasar.
A ranar Talata Leicestern za ta karbi bakuncin Sevilla a wasansu karo na biyu na zagayen kungiyoyi 16 na Kofin Zakarun Turai, wanda kungiyar ta Spaniya ta ci na farko 2-1.