U 20: Zambia ta dauki kofi bayan ta doke Senegal 2-0

Filin wasa na kasa na National Heroes da ke Lusaka Hakkin mallakar hoto KENNEDY GONDWE
Image caption An yi wasan na karshe ne a babban filin wasa na National Herores Stadium da ke Lusaka, a Zambian

Mai masaukin baki Zambia ta dauki kofin kasashen Afirka na gasar kwallon kafa ta 'yan kasa da shekara 20, bayan ta doke Senegal da ci 2-0, a Lusaka, ranar Lahadi.

Minti 15 da shiga fili sai Daka P. Ya fara daga ragar bakin, kafin Chilufya E. ya biyo baya da ta biyu a minti na 35.

Wannan shi ne karo na biyu a jere da Senegal take zuwa wasan karshe, kuma kamar Zambian ba ta taba cin kofin ba.

Senegal ta yi nasarar zuwa wasan na karshe ne bayan ta doke Guinea 1-0 ranar Alhamis.

Ita ma Zambia ta kai wasan na karshe ne bayan ta ci Afirka ta Kudu 1-0 a wasan kusa da karshe, ranar Laraba.

A shekara ta 2015 ne Senegal ta fara zuwa wasan karshe inda Najeriya ta doke ta

Tun da farko a wasan da aka yi na neman matsayi na uku a gasar, a ranar Lahadin, Guinea ta ci Afirka ta Kudu 2-1.

Duka kasashe hudun da suka kai wannan mataki sun samu gurbin gasar Kofin Duniya ta 'yan kasa da shekara 20 da za a yi a Koriya ta Kudu a watan Mayu.