Liverpool ta jaddada zama ta hudu bayan cin Burnley 2-1

Georginio Wijnaldum a lokacin da ya ci Burnley Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Georginio Wijnaldum ya ci kwallo biyu a wasansa biyu da ya gabata a Liverpool

Liverpool ta kara jaddada zamanta a cikin kungiyoyi hudu na farko na gasar Premier bayan da a gidanta, ta sha da kyar a hannun Burnley da ci 2-1, ta hada maki 55, a wasan mako na 28.

Bakin ne suka fara jefa kwallo a ragar Liverpool din ta hannun Ashley Barnes, minti bakwai kacal da fara taka leda, a wasan na mako 28.

Ana dab da tashi daga kashin farko na wasan ne sai Georginio Wijnaldum ya farke wa Liverpool kwallon.

Emre Can ne ya ci wa Liverpool kwallon da ta ba ta nasara a wasa biyu a jere, a minti na 61, wadda ita ce ta hudu da dan wasan ya ci a bana.

Wasan dai bai yi wani armashi ba sosai ko da yake nasarar ta ba wa kungiyar ta Jurgen Klopp, damar yi wa Arsenal wadda ke bi mata baya, tazara da maki biyar.

Yanzu Liverpool ta ci wasan Premier 16 Premier kenan a bana; daidai da yawan wasan da ta ci gaba daya a kakar da ta wuce ta 2015-16.

Burnley, wadda har yanzu ba ta ci wani wasa ba a waje a bana, tana matsayi na 12 a tebur, da maki 31, kuma a wasanta na gaba ranar Asabar 18 ga watan Maris, za ta ziyarci Sunderland wadda ke neman tsira, da karfe 4:00 na yamma agogon Najeriya.

A ranar Lahadi 19 ga watan Maris, da karfe 5:30 na yamma agogon Najeriya, Liverpool za ta bakunci Manchester City.