Tottenham da Ingila na fargabar raunin Harry Kane

Harry Kane a wasan Ingila
Image caption Harry Kane, mai shekara 23, wanda ya ci kwallo 24 a bana, ya bar filin wasan ne da sandar guragu.

Mai yuwuwa dan wasan Ingila da Tottenham Harry Kane ya sake yin jinyar raunin idon kafa, kamar yadda ya yi fama a farkon kakar nan, jinyar da ta hana shi wasan Premier biyar, kamar yadda kociyan Tottenham Mauricio Pochettino yake fargaba.

A jiya Lahadi ne Kane ya ji raunin a wasan dab da na kusa da karshe na cin Kofin FA, wanda Tottenham ta lallasa Milwall 6-0, raunin da ya sa aka cire dan wasan minti bakwai da fara taka leda.

Kociyan nasa ya ce raunin ya yi kama da wanda ya ji a wancan lokacin da suka hadu da Sunderland, kuma a kafar da ya ji wancan din, kociyan ya ce a yau ne suke tsammanin sanin girman raunin.

Kane, mai shekara 23, wanda ya ci kwallo 24 a bana, ya bar filin wasan ne da sandar guragu.

Kane ne ya zama gwarzon dan wasan Premier na watan Fabrairu, kuma ba dan wasan da ya ci yawan kwallo 19 da ya ci a gasar Premier a bana, sai Romelu Lukaku na Everton.

Raunin nasa zai iya kasancewa wata matsala ga kociyan tawagar Ingila Gareth Southgate, wanda a ranar Alhamis, zai bayyana sunan 'yan wasan da ya zaba wadanda za su buga wasan gwaji da sada zumunta da Ingila za ta yi da Jamus ranar 22 ga watan Maris da kuma wasan neman gurbin gasar Kofin Duniya da Lithuania kwana hudu bayan wasan Jamus din.