Kofin FA: Karon battar Man Utd da Chelsea

Manchester United ta dauki kofin FA na bara Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester United ta doke Crystal Palace 2-1 a wasan karshe na bara inda Jesse Lingard da Juan Mata suka ci mata kwallo

A ranar Litinin din nan ne za a fitar da jadawalin wasan kusa da karshe na gasar cin Kofin FA, bayan karon-battar Chelsea da Manchester United a Stamford Bridge.

Za a fara wasan ne na matakin dab da na kusa da karshe da karfe 8: 45 agogon Najeriya.

Biyar daga cikin manyan kungiyoyin Premier shida har yanzu suna cikin gasar, bayan da Arsenal ta doke Lincoln City , ita kuma Tottenham ta fitar da Millwall.

Kungiyoyin biyar sun dauki Kofin na FA gaba dayansu sau 44, wanda ya hada da 12 daga cikin 15 da ya gabata.

Za a yi wasannin na kusa da karshe ne duka biyun a filin Wembley a karshe mako tsakanin ranakun 22 da 23 na watan nan na Afrilu.