Kofin FA: Karon battar Man Utd da Chelsea

'Yan wasan Manchester United Jesse Lingard da Juan Mata dauke da Kofin FA na bara Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Man Untd ta doke Crystal Palace 2-1 a wasan karshe na bara inda Jesse Lingard da Juan Mata suka ci mata kwallayen

A ranar Litinin din nan ne za a fitar da jadawalin wasan kusa da karshe na gasar cin Kofin FA, bayan karon battar Chelsea da Manchester United a Stamford Bridge.

Za a fara wasan ne na matakin dab da na kusa da karshe da karfe 8: 45 agogon Najeriya.

Biyar daga cikin manyan kungiyoyin Premier shida har yanzu suna cikin gasar, bayan da Arsenal ta doke Lincoln City , ita kuma Tottenham ta fitar da Millwall.

Kungiyoyin biyar sun dauki Kofin na FA gaba dayansu sau 44, wanda ya hada da 12 daga cikin 15 da ya gabata.

Za a yi wasannin na kusa da karshe ne duka biyun a filin Wembley a karshe mako tsakanin ranakun 22 da 23 na watan nan na Afrilu.