Kofin FA: Man Untd na fuskantar matsalar dan gaba

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wayne Rooney na daya daga cikin 'yan wasa 8 da suka ci wa United kwallo a gasar Kofin FA a bana

Kyaftin din Man United Wayne Rooney ba ya cikin wadanda za su buga wasanta na dab da na kusa da karshe na Kofin FA, da Chelsea, yau Litinin, abin da ya sa kungiyar ta zama ba ta da wani sanannen dan gaba.

Rooney ya yi karo ne da Phil Jones a lokacin atisaye inda ya ji rauni a kafa, yayin da shi kuma Zlatan Ibrahimovic ya fara hukuncin hana shi wasa uku na laifin gula da ya yi wa dan wasan Bournemouth Tyrone Mings a fuska.

Haka su ma 'yan wasan gaba na kungiyar Anthony Martial da Marcus Rashford ba sa cikin jerin 'yan wasan na United.

Shi kuwa kociyan Chelsea Antonio Conte dukkanin 'yan wasansa suna nan, ba shi da wata matsala.

Ba a dai san yanayi da tsananin raunin na Rooney ba, amma dai kyaftin din na Ingila ya kammala atisayen, kuma a ranar Litinin din nan za a duba raunin.

A da dai an sa ran Rooney, mai shekara 31, zai yi wasan, saboda ba a je Rasha da shi ba, wasan Kofin Europa da Rostov ranar Alhamis.

Ana tsammanin a ranar Alhamis, kociyan Ingila Gareth Southgate zai bayyana sunan Rooney a cikin 'yan wasan da za su buga wa Ingila wasan gwaji da sada zumunta da Jamus ranar 22 ga watan Maris, da kuma wanda za su yi na neman gurbin gasar Kofin Duniya da Lithuania a Wembley ranar 26 ga watan na Maris.

A watan Janairu Rooney ya zama dan wasan da ya fi ci wa United kwallo a tarihi, inda ya shafe tarihin da Sir Bobby Charlton ya kafa na wannan bajinta.

Sai dai tun daga ranar 1 ga watan Fabrairu sau daya ya yi wasa, kuma a watan da ya gabata ya ki karbar tayin da aka yi masa na komawa China, domin ya kammala kakar wasa ta bana a Old Trafford.