An haramta wa wani likitan Rasha shiga harkokin wasanni har abada.

Samfurin abubuwan da ake gwada wa na 'yan wasa don gano ko sun yi amfani da abubuwan kara kuzari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An zargi Dakta Sergei Portugalov da samarwa da kuma ba wa 'yan wasa wasu abubuwa da aka hana amfani da su

An haramta wa wani likitan Rasha shiga harkokin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle har abada, saboda hannun da yake da shi a laifin amfani da abubuwan kara kuzari da 'yan wasan kasar suka yi.

Kotun harkokin wasanni ta duniya (Cas) ta ce akwai cikakkiyar sheda da ta nuna Dakta Sergei Portugalov ya ba wa 'yan wasa abubuwan kara kuzari.

Rahotan hukumar yaki da amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni ta duniya na 2015, ya ce likitan yana da hannu dumu-dumu wajen kokarin boye sakamakon gwajin 'yan wasan da aka gano sun yi amfani da abubuwan kara kuzari, domin ba shi wani kaso na abin da suka ci a wasa.

Rahoton hukumar ta Wada na bara ya ce sama da 'yan wasan Rasha 1,000 ne maza da mata suka amfana da yadda jami'an kasar suka ba su abubuwan kara kuzari.

Akan hakan ne hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta haramta wa 'yan wasan Rasha shiga wasanni, har sai ta gamsu da yadda ake gudanar da ayyukan hana amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni a kasar.

Kuma kawo yanzu manyan jami'ai a hukumar ta duniya sun fara nuna gamsuwa da matakan da rashan take dauka na dawo da kimarta.