Shirin wasannin Commonwealth a Durban ya gamu da cikas

Jami'an gwamnatin Afirka ta Kudu da na gasar Commonwealth
Bayanan hoto,

Gasar ta wasannin ta Commonwealth ta 2022 da za ta kasance ta farko da aka yi a Afirka

Bisa ga dukkan alamu ba za a gudanar da gasar wasannin kungiyar Commonwealth ta 2022 a birnin Durban na Afirka ta Kudu, ba kamar yadda BBC ta fahimta.

Ana ganin birnin bai cika ka'idojin da hukumar wasannin ta gindaya ba, kuma ana sa ran nan gaba a ranar Litinin din nan ne za a bayar da sanarwa a kai.

A shekara ta 2015 ne aka ba wa birnin damar karbar bakuncin gasar, saboda shi kadai ne ya gabatar da bukatarsa ta karba, wanda da zai kasance birnin Afirka na farko da ya karbi bakuncin gasar.

Birnin Liverpool ya nuna sha'awarsa ta karbar gasar, sakamakon alamun da aka gani na gazawar birnin na Durban.

Mai magana da yawun hukumar birnin na Liverpool ya ce sun ji rade-radin cewa birnin na Afirka ta Kudu ba zai iya karbar gasar ta 2022 ba, saboda haka tuni suka nuna wa gwamnati sha'awarsu ta karbar bakuncin.

A shekara ta 1930 aka fara gudanar da gasar, kuma daga nan ake yinta duk bayan shekara hudu, inda 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle daga sama da kasashe 50, yawanci wadanda Birtaniya ta mulka suke halarta.

A watan da ya gabata ne ministan wasanni na Afirka ta Kudu Fikile Mbalula ya nuna alamun birnin na Durban kila ba zai iya karbar bakuncin gasar wasannin ta Commonwealth ta 2022 ba saboda matsalar.