FA za ta binciki Millwall kan cin zarafin dan wasan Tottenham Son

Son da abokan wasansa na murnar kwallon da ya ci Millwall Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Son tare da abokan wasansa na murnar cin kwallo ta uku da ya zura a ragar Millwall

Hukumar kwallon kafar Ingila za ta yi bincike, kan wakokin wariyar launin fata da magoya bayan Millwall, suka rika yi wa dan wasan Tottenham Son Heung-min lokacin da suka doke Millwall 6-0 a wasan Kofin FA.

Magoya bayan Millwall din dai sun yi ta rera wakokin wariyar launin fatar ne ga dan wasan, dan Kasar Koriya ta kudu, a yayin karawar ta wasan dab da na kusa da karshe.

Kociyan Millwall din dai, Neil Harris ya ce duk wanda aka samu da laifi cikin magoya bayan kungiyar zai fuskanci mummunan hukunci.

Ya kara da cewa"wannan ai abin kunya ne ma a yi magana a kansa"

Son din dai ya ci kwallo uku, a wasan da ya bai wa Tottenham damar zuwa wasan kusa da karshe a gasar ta cin Kofin FA.

Kungiyar ta Premier ta ce, za ta bayar da duk wani hoton bidiyo da zai taimaka wajen gano wadanda ake zargin

Daman Millwall na fuskantar bincike daga Hukumar ta FA a kan korafin da kungiyar Leicester ta yi kan magoya bayanta a wasan da suka yi nasara a wasan gasar na baya.

Kungiyar ta Millwall dai ta ce tana kan gaba wajen yaki da dabi'ar wariyar launin fata, kuma za ta ci gaba da yin hakan.

Kungiyar ta kara da cewa tana taimaka wa hukumar kwallon kafar a binciken da take gudanarwa, kuma ba za ta ce komai ba sai an gama binciken.

An dai girke jami'an 'yan sanda a wajen harabar filin wasan na White Hart Lane inda aka yi wasan ranar Lahadi, kafin a tashi daga wasan.

Inda magoya bayan kungiyoyin biyu suka fara cece-kuce, har ta kai su ga jifan juna da kwalabe, da kuma duwatsu