Kun san dan wasa mafi shekaru da ya zura kwallo a raga?

Kazuyoshi Miura (a tsakiya) lokacin da ya ci kwallon Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kazuyoshi Miura (a tsakiya) ya fara wasan kwararru a shekarar 1986

Kazuyoshi Miura ya zama dan wasan farko na kwallon kafa mai shekara 50 da ya ci kwallo a gasar lig ta kasar Japan, inda ya kawar da tarihin da ya kafa a baya na wannan bajinta.

Miura ya ci wa kungiyarsa ta Yokohoma FC kwallo ne a wasan gasar rukuni na biyu na Japan, inda suka doke kungiyar Thespa Kusatsu da ci 1-0, yana mai shekara 50 da kwana 14, inda ya kawar da tarihin da ya kafa a baya.

Tsohon dan wasan na tawagar kasar Japan ya ce yana da sha'awar ganin kawai ya zura kwallo a raga.

Miura, wanda ya ci wa kasarsa Japan kwallo 55 a wasa 89, ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar Yokohama FC a watan Janairu.

Dan wasan ya fara wasan kwararru ne a kungiyar Santos ta Brazil a shekarar 1986, sannan ya yi Genoa ta Italiya na dan lokaci da kuma Dinamo Zagreb ta Croatia a shekarun 1990.

Dan wasan na gaba ya koma kungiyar Yokohama FC ne a shekarar 2005 yana da shekara 38.

Sai dai kuma hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ba ta iya tabbatar ko Miura shi ne dan wasa mafi shekaru da ya zura kwallo a raga a wata gasar kwallon kafa ba.

Dan wasa mafi tsufa da yake da wannan tarihi a wata karawa ta kasa da kasa shi ne Billy Meredith, wanda ya ci wa Wales kwallo a karawarta da Ingila lokacin yana da shekara 45 da kwana 73, a 1919.

Haka kuma ya ci wa Manchester City a wasanta da Brighton a gasar Kofin FA yana da shekara 49 da kwana 208 a 1924.