Kofin Zakarun Turai: Leicester da Sevilla

Jamie Vardy lokacin da ya ci Seville Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Jamie Vardy ne ya ci wa Leicester kwallonta a gidan Seville

A ranar Talata ne Leicester za ta yi wasanta na biyu na zagayen kungiyoyi 16 na Zakarun Turai, inda za ta yi kokarin galaba a kan Sevilla wadda ta doke ta 2-1 a Spaniya.

Wasan na biyu shi ne na farko na sili-daya-kwale da kungiyar za ta yi a gida na babbar gasar Turai.

Karon farko da aka doke su, shi ne wasan karshe na Claudio Ranieri a matsayin kociyan kungiyar ta Leicester kafin a kore shi, wata tara da ya daukar musu kofin Premier.

Tun daga wannan lokacin sun ce wasansu biyu na Premier, inda suka doke Liverpool 3-1, kamar yadda suka yi wa Hull City, a karkashin jagorancin Craig Shakespeare, yana rikon kwarya, wanda yanzu kuma aka tabbatar masa da matsayin cikakken kociya har karshen kakar nan.

A daya wasan na Zakarun na Turai na Talata, Juventus wadda a wasan farko ta ci FC Porto 2-0, za ta karbi bakuncin kungiyar ta Portugal.

Jagorar ta Serie A, wadda ta dauki Kofin na Zakarun Turai a 1996 rabon da ta kai wasan dab da na kusa da karshe na gasat tun 2015, inda Barcelona ta fitar da su 3-1 a wasan karshe.