Man Utd ta so raunata Hazard ne - Antonio Conte

Antonio Conte ya ji dadin kokarin da Eden Hazard ya yi Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Antonio Conte ya ce 'yan wasan Manchester United sun so fitar da Eden Hazard ne kawai

Kociyan Chelsea Antonio Conte ya zargi Man United da niyyar raunata Eden Hazard a lokacin wasan dab da na kusa da karshe da suka fitar da United din daga gasar Kofin FA da ci 1-0 a Stamford Bridge.

Kociyan ya ce a minti 20 zuwa minti 25 Hazard ya kasa samun damar da zai taka leda yadda ya kamata, saboda sun takura masa.

Conte ya kara da cewa ba abin da 'yan Manchestern suke yi sai dukansa kawai, kuma shi kadai suka rika yi wa haka.

Alkalin wasa ya kori Ander Herrera daga wasan a sanadiyyar ketar da ya yi wa Hazard sau biyu, yayin da shi kuma Marcos Rojo ya taka dan wasan na Belgium bayan korar.

Kwallon da N'Golo Kante ya ci wa Chelsea a minti na 51 ita ba wa jagorar ta Premier damar zuwa wasan kusa da karshe, wanda za ta yi da Tottenham a Wembley cikin watan Afrilu.

Conte ya yi sa-in-sa da takwaransa Jose Mourinho, jim kadan bayan alkalin wasa ya kori Herrera, sakamakon takun da aka ce Rojo ya yi wa Hazar, wanda har ta kai sai da mataimakin alkalin wasa na waje Mike Jones ya shiga tsakaninsu.

Yanzu dai dan wasan bayan na Argentina zai jira ya ga ko hukumar kwallon Ingila za ta dauki mataki a kansa bayan da alkalin wasa Michael Oliver ya sanya sunansa a cikin rahoton yadda wasan ya kasance.

Conte ya ce wannan dabarar ta neman fitar da dan wasan da kuke gani zai zama hadari a gareku, ba a yinta a wasa yanzu. Ya ce wannan ba wasan kwallon kafa ba ne.

Nasarar ta ranar Litinin ta kara ba wa Chelsea wadda ke da tazarar maki 10 a saman teburin Premier, damar daukar kofuna biyu na Ingila.