Kante ne na daya a duniya - Lampard

N'Golo Kante dan wasan Faransa da Chelsea
Image caption Masu fashin bakin wasan kwallon kafa na ta yaba wa N'Golo Kante

Dan wasan Chelsea N'Golo Kante shi ne na daya yanzu a duniya a tsakanin takwarorinsa 'yan wasan tsakiya, in ji tsohon dan wasan kungiyar ta Blues Frank Lampard.

Lampard ya bayyana Kante a matsayin jigo ko karfin Chelsea a kokarin da take yi na daukar kofuna biyu na Ingila.

Kante, mai shekara 25, shi ne ya ci wa kungiyar ta Antonio Conte bal din da ta sa ta fitar da Manchester United daga gasar Kofin FA, ranar Litinin, ta kai wasan kusa da karshe.

Kuma ita ce ta biyu da ya ci a bana, sannan dukkaninsu ya zura su ne a ragar Manchester United.

Dan wasan na kasar Faransa, wanda Chelsea ta sayo daga Leicester a bazarar da ta wuce a kan fan miliyan 30, ya kasance kan gaba cikin 'yan wasan kungiyar wadda ta bayar da tazarar maki 10 a teburin na Premier.

Haka shi ma tsohon dan wasan baya na Manchester United Phil Neville, wanda yake yi wa BBC fashin baki a kan wasanni tare da Alan Shearer da Lampard, ya bayyana dan wasan na Faransa da cewa, a yanzu shi ne dan wasan tsakiya mafi tasiri a Turai baki daya.

Neville ya kara da cewa, shi bai ga dan wasan da yake da tasiri a kan kungiyar ta Chelsea ba kamarsa, ya ce shi ne lamba 6, shi ne lamba 8, shi ne kuma 10.

Shi ma tsohon dan wasan baya na Arsena Martin Keown wanda ke yi wa BBC fashin baki, da yake bayyana gwanin dan wasansa a karawar ta Chelsea da United, ya ce, gwanin dan wasa? ''A a ai sai dai a kira shi gwanayen 'yan wasa. Saboda yana ko'ina.''