Tennis: Jamie Murray ne kawai dan Birtaniya da ya rage a gasar India

Andy Murray da Dan Evans Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Andy Murray (a dama) ya rasa damar karawa da dan uwansa Jamie, bayan da aka doke shi da Dan Evans a wasan 'yan bibbiyu

Jamie Murray ya kasance dan wasan tennis daya tilo na Birtaniya, da ya rage a babbar gasar tennis ta India, bayan da aka fitar da dan uwansa Andy Murray da Dan Evans daga wasan 'yan bibbiyu.

Ba zato ba tsammani Vasek Pospisil ya yi waje da gwanin wasan tennis din na daya a duniya Andy Murray, a wasan daidai, yayin da Evans ya yi rashin nasara da ci 6-4 6-3 a hannun Jean-Julien Rojer da Horia Tecau.

Yanzu wadanda suka yi nasarar za su fafata da Jamie Murray da Bruno Soares a wasan dab da na kusa da karshe na gasar ta India.

Jamie Murray da Soares sun yi nasara da ci 7-6 (7-3) 6-3 a kan Treat Huey da Max Mirnyi.

A zagaye na biyu ne na wasan 'yan daidai aka yi waje da Andy Murray da Evans da Kyle Edmund, yayin da gwana ta daya a wasan na tennis a Birtaniya Johanna Konta, wadda ta doke 'yar uwarta 'yar Birtaniya Heather Watson a zagaye na biyu, ita ma aka yi waje da ita a zagaye na uku.