Kungiyar Boa Esporte ta Brazil ta dauki golan da ya kashe budurwarsa

Bruno Fernandes Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sa ran Brazil za ta je da Bruno Fernandes gasar Kofin Duniya ta 2014

Kungiyar Boa Esporte ta Brazil ta dauki mai tsaron raga Bruno Fernandes, wanda aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari kan kisan tsohuwar farkarsa, kuma ya ba wa karnukansa gawarta suka cinye.

An yankewa Fernandes, wanda aka fi sani da suna Bruno a Brazil, hukuncin zaman gidan kaso na shekara 22, saboda halaka farkar tasa Eliza Samudio a shekara ta 2010.

A watan da ya wuce ne aka saki tsohon golan na kungiyar Flamengo bisa wasu ka'idoji na shari'a.

Jama'a da dama a Brazil sun yi suka, kan daukar dan wasan da kungiyar ta yi, lamarin da ya jawo zanga-zangar magoya baya da kuma janyewar kamfanoni da dama masu daukar nauyin kungiyar ta Boa Esporte.

A yayin taron 'yan jarida na kan daukar tasa, Bruno, wanda aka saki har zuwa lokacin da za a yi zaman daukaka karar da ya yi, ya ki amsa tambayoyi game da kisan Ms Samudio, tsohuwar farkar tasa, kuma uwar dansa.

Ko da yake ba a ga matar ba, amma dan uwanta ya gaya wa kotu cewa an ba wa karnuka gawar ta ne suka cinye.

Masu gabatar da kara sun ce Bruno ya kashe ta ne saboda ta nemi ya biya ta kudin kula da dansu.

A lokacin shari'ar dan bal din ya amince cewa ya san an kashe Ms Samudio kuma an ba wa karnuka gawarta, amma ya musanta cewa shi ya sa aka kashe ta.