FA ta gurgunta kwallon mata a baya - Glenn

'Yan wasan Ingila mata suna murnar zama na uku a gasar Kofin Duniya ta 2015 a Canada Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ingila ta doke Jamus, ta zama ta uku a gasar cin Kofin Duniya ta 2015 ta kwallon mata da aka yi a Canada

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, Martin Glenn ya ce, hukumar ba ta kula da wasan kwallon mata ba, hasali ma ta gurguntar da wasan a baya.

A shekara ta 1921 hukumar ta haramta yin wasan na mata a filayen kwallon da ake gasar lig a Ingila, kuma FA din ba ta yadda ta dawo da wasan karkashin ikonta ba har sai a shekarar 1993.

Glenn wanda ya ce har sai da suka hana ma yin wasan a filayen da ke karkashin ikon FA, kuma sun yi jinkiri wajen amincewa da wasan, a yanzu suna kokarin magance duka wannan nakasu da suka yi wa wasan kwallon kafar matan.

A ranar Litinin hukumar kwallon kafar ta Ingila ta bullo da wasu tsare-tsare na linka yawan matan da ke wasan kwallon kafa har sau biyu nan da shekara ta 2020.

Tawagar 'yan wasan kwallon mata ta Ingila ta yi ta uku ne a gasar cin Kofin Duniya da aka yi a 2015, kuma za ta shiga gasar cin Kofin Kasashen Turai da za a yi a bazarar nan a Holland.

FA ta ce za ta so karbar bakuncin manyan wasanni na kwallon kafa na duniya na mata a shekarun da ke tafe domin karfafa wa 'yan gaba guiwa a wasan.