FA ta tuhumi Man United kan 'yan wasanta

Referee Michael Oliver was surrounded by several Manchester United players after sending off midfielder Ander Herrera Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption 'Yan wasan Manchester United sun baibaye alkalin wasa Michael Olive lokacin da ya kori Ander Herrera

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi Manchester United da laifin kasa tsawatar wa 'yan wasanta a lokacin wasan da Chelsea ta doke ta 1-0,na dab da na kusa da karshe na Kofin FA ranar Litinin.

Tarin 'yan wasan na United dai sun kewaye alkalin wasan Michael Olive bayan da ya kori dan wasansu na tsakiya Ander Herrera, minti 10, kafin tafiya hutun rabin lokaci.

A sanarwar da hukumar FA ta fitar ta ce Manchester United din tana da dama har zuwa karfe 6:00 na dare agogon GMT, ranar Juma'a ta yi bayani.

Alkalin ya kori Herrera, dan wasan na tsakiya na Spaniya bayan da ya yi wa dan wasan gaba na Chelsea Eden Hazard keta a karo na biyu.

Sai dai kuma FA din ba ta dauki wani mataki akan Marcos Rojo ba a kan ketar da ake ganin shi ma ya yi wa Hazard din can gaba a wasan, abin da alkalin wasan ya ce ya gani kuma ya dauki matakin da yake ganin ya dace a lokacin.