Lukaku ya yi watsi da makudan kudaden Everton

Romelu Lukaku Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Romelu Lukaku ya ci wa Everton kwallo 19 a bana

Dan wasan gaba na Everton Romelu Lukaku ya yi watsi da tayin da kungiyar ta yi masa na ba shi kwantiragin da za ta rika biyanshi kudin da ba ta taba biyan wani dan wasa ba a tarihi.

Kafin yanzu dai kungiyar ta Premier tana da kwarin guiwa cewa dan wasan na Belgium zai rattaba hannu a sabuwar yarjejeniya ta tsawon shekara biyar da ita, wadda za ta rinka biyansa albashin fam dubu 140 a duk mako.

A baya wakilin Lukakun, Mino Raiola, ya ce yana da tabbaci kashi 99.9 cikin dari dan wasan mai shekara 23 zai ci gaba da zama a Everton.

Sai kuma a yanzu kwatsam sai, dan wasan ya gaya wa kungiyar ba shi da niyyar tsawaita kwantiragin da zai yi shekara biyu.

Shi dai Lukaku ya sha nuna sha'awarsa ta wasa a gasar Kofin Zakarun Turai, abin da ya sa ma har ake rade-radin komawarsa kungiyarsa ta da Chelsea, wadda ta sayo shi daga Everton akan fan miliyan 28 a 2014.

Kila Everton ta yi kokarin shawo kan dan wasan ya tsaya, idan kuma ba haka ba, to za ta iya neman kudin da ya kai fan miliyan 60 daga duk kungiyar da za ta nemi dan wasan wanda ya ci kwallo 19 a bana.