Zakarun Turai: Ba ma son haduwa da Leicester - Buffon

Gianluigi Buffon Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Buffon ya taimaka wa Juventus ta dauki kofin Serie A sau biyar a jere, kuma yanzu ta ba da tazarar maki 8 a gasar da take harin kofi na 6 a jere

Kyaftin kuma golan Juventus Gianluigi Buffon ya ce ba sa son a hada su da Leicester City a wasan dab da na kusa da karshe na Kofin Zakarun Turai.

Zakarun na Italiya sun doke Porto 3-0 jumulla, wasa gida da waje, suka kai wasan dab da na kusa da karshe, yayin da Leicester ta yi nasarar zuwa matakin, bayan da ta yi galaba a kan Sevilla a ranar Talata da ci 3-2 jumulla, wasa gida da waje.

Kyaftin din na tawagar Italiya, mai shekara 39, ya ce ba sa kaunar a hada su da Leicester saboda kungiya ce mai hadari da kuma sha'awar yin wasa, wadda za ta iya haddasa wa abokan karawar matsala.

Real Madrid da zakarun Spaniya Barcelona da kuma zakarun Jamus Bayern Munich na daga cikin kungiyoyin da tuni suka yi nasarar zuwa matakin wasan dab da na kusa da karshen.

Yawancin masu fashin bakin wasan sun sa Juventus a matsayin ta hudu a jerin wadanda suke ganin za su iya daukar kofin na Zakarun Tura, yayin da ba sa sanya Leicester din cikin wannan jeri.