An rufe filin wasan FC Rostov bayan korafin Mourinho

Filin wasan FC Rostov, Olimp-2 Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rostov za ta bar filin Olimp-2 bayan gasar Kofin Duniya ta 2018 a Rasha

Sati daya bayan da Jose Mourinho ya soki filin wasan FC Rostov ta Rasha, hukumar wasan Premier ta kasar ta haramta wa kungiyar yin wasannin gasar kasar saboda rashin kyawun filin.

Manchester United ta yi kunnen-doki 1-1 a filin wasan kungiyar, Olimp-2 Stadium, a wasansu na farko na zagayen kungiyoyi 16 na kofin Europa, ranar Alhamis da ta wuce.

A lokacin da kocin na United ya je yana duba filin kafin karawar tasu, ya ce, ya kasa yarda cewa wai a wannan fili za su yi wasan, in har ma za a iya kiransa fili.

Hukumar gasar Premier ta Rasha ta gaya wa BBC cewa za a sake zuwa duba filin na Rostov ranar 24 ga watan Maris, yayin da za ta yi wasanta na gida na gaba a ranar 31 ga watan Maris, da FC Krasnodar.

Sai dai hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa, ta ce filin ya cancanci a yi wasan gasar Europa a cikinsa, amma kuma ita hukumar gasar lig din Rasha ta ce tana da dokoki irin nata na daban.

A ranar Alhamis ne Manchester United da Rostov za su yi wasansu na biyu na gasar ta Europa a Old Traffor.

Bayan filin na Rostov, hukumar gasar Premier ta Rasha ta kuma rufe filin wasan kungiyar Rubin Kazan ma.