Ci za mu nema ba kariya ba - Guardiola

Sergio Aguero lokacin da ya zura kwallo a ragar Monaco Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Aguero ya ci wa City kwallo 6 a wasa 5 da ya yi a karshen nan, da suka hada da biyun da ya zura wa Monaco ranar 21 ga watan Fabrairu

Kocin Manchester City Pep Guardiola, ya ce ba za su koma baya su nemi kare cin da suka yi wa Monaco ba, a karawa ta biyu ta neman gurbin dab da na kusa da karshe na gasar Zakarun Turai, a ranar Laraba.

Manchester City ta doke kungiyar ta Faransa 5-3 a Etihad ranar 21 ga watan Fabrairu.

Monaco ta zura kwallo 123 a raga gaba daya a bana, kuma Guardiola yana ganin za su yi wawanci idan har suka bar 'yan wasan suka rika kai musu hari, yana mai kari da cewa abin da ya fi kawai shi ne; ''Mu ci kwallo.''

Kociyan dan Spaniya ya ce idan kungiya ta ci kwallo da yawa, kuma ta ce wai za ta koma baya ne kawai ta tsaya tana kare kanta, to ka kashe kanka kawai. Abin da ya kamata kawai shi ne ka rika kai hari.

Guardiola, wanda zai jagoranci wasansa na 100 cif a gasar Kofin Turai ranar Laraba, ba shi da wata fargaba ta 'yan wasa da ke jinya, a karawar ta Faransa.

Dan wasansa na gaba Gabriel Jesus da na tsakiya Ilkay Gundogan su kadai ne manyan 'yan tamlarsa da ke jinya.

Ana sa ran kyaftin din kungiyar tasa Vincent Kompany kila ya shiga wasan a karo na biyu kenan tun watan Nuwamba.